Taimako ga wadanda yakin Boko Haram ya shafa | Siyasa | DW | 14.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taimako ga wadanda yakin Boko Haram ya shafa

Kwamtin da gwamnatin Najeriya kafa domin tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa da su, ya fara raba kudaden agaji ga wadanda musamman suke samun kulawar likita asibitoci.

Kwamtin da da gwamnatin Najeriya kafa domin tallafawa wadanda rikicin Boko haram ya rutsa da su, ya fara raba kudaden agaji ga al'ummomin a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, musamman wadanda suke samun kulawar likita asibitocin shiyyar. Wannan kwamiti dai an kafashi ne bayan kwamitin kula da tattara kudaden tallafi ga wadan da rikicin Boko Haram ya rutsa da su a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya karkashin jagorancin Janar T. Y. Danjuma ya mkia rahoton sa, bayan tattara makudan kudade. Manufar wannan kwamiti shi ne duba wadanda suka cancanci samun wanna tallafi, musamman mata da yara da kuma wadanda ke kwance a asibitoci da ciobiyoyin kula lafiya da ya kamata a samar musu da kayan aiki isassu da zasu taimakawa wadanda suka samu raunuka kuma suke bukatar kulawar likita.

Kwamitin ya ziyarci jihar Gombe, inda aka raba Naira miliyan 40 ga manyan asibitoci da ke Gombe wato asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da kuma asibitin kwararru wadanda suke jiyyar mutane da suka samu munanan raununa sandiyyar hare-haren bama-bamai a jihar.

Shugaban kwamitin Farfesa Victor Ochehce ya yi karin bayani kan wannan shiri na su da kuma inda zasu fi maida hankali.

“Ya ce makasudin zuwanmu shine hada kai da gwamnatin jiha, tare da hukumomin da ke kula da wadanda rikicin ya rutsa da su musamman cibiyoyin kiwaon lafiya, kuma wannan kwamiti zai fi maida hankali ne ga mata da yara, musamman wadanda suka rasa mazajensu wanda ala tilas suka koma masu kula da iyalan su”.

Haka kuma kwamtin zai raba wasu kudaden ga irin wadannan matan da suka rasa mazajen su sandiyyar irin wadannan hare-hare, domin taimaka musu kula da iyalai da ke gaban su.

Na ziyarci asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke nan Gombe, na kuma tattauna da wasu daga cikin wadanda ke samun kulawar likita wadanda suka samu tallafi daga gwamnatin jihar da kuma wasu ‘yan siyasa. Ga ma abinda suke cewa.

Babban daraktan asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke nan Gombe Dr Abubakar Sa'idu ya bayyana kudaden da aka ware musu sun kai miliyan 20, kuma za su sayi kayayyakin aiki don ci gaba da taimakawa marassa lafiya.

Sai dai yace akwai bukatar kara yawan wadannan kudade. Akwai dai masu neman wannan kwamiti ya shigar da wadanda jami'an tsaro suka hallaka ko jikkatasu ba tare da hakkin shari'a ba da suma iyalan su ke neman tallafi kamar yadda Aminu Turaki, wani da jami'an tsaro suka hallaka iyalinsa ba gaira ba dalili ya shaida min.

Sauti da bidiyo akan labarin