Tahirin cutar Zika | Amsoshin takardunku | DW | 08.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tahirin cutar Zika

Cutar Zika mafi girma da aka samu a wajen kasashen Afirka ta kasance wadda ta bulla a Brazil a shekara ta 2015.

Kamar yadda hukumar lafiya ta nunar cutar Zika ta taba bulla a wasu kasashen Afirka. Amma yanzu haka cutar tun lokacin da ta bulla a Brazil ake neman matakan ganin an shawo kanta.

Masani kiwon lafiya sun gano cutar a karion farko a shekarar 1947 cikin yankin gabashin Afirka. Cutar tana cikin wadanda sauro yake yadawa. Tun lokacin da cutar ta Zika ta bulla a Brazil a shekara ta 2015 an tabbatar ta kama mutane 49, yayin da ake duba wasu 59 da ake zaton cutar ta kama su.