Tagwayen bama-bamai sun fashe a Gombe | Labarai | DW | 16.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tagwayen bama-bamai sun fashe a Gombe

Minti biyu ne tsakanin fashewar bam na farko da na biyu, kuma harin ya afku ne yayin da kasuwar ta cika da masu sayayyar Sallah.

Ana fargabar mutane da dama sun mutu, wasu kuma sun jikata bayan tashin wasu tagwayen Bama-Bamai a babbar kasuwar Gombe a dai dai lokacin da jama’a ke hada-hadar sayayyan kayan Sallah.

Bam na farko dai ya tashi ne da misalin karfe biyar da minti 12 inda na biyu ya tashi da misalin karfe biyar da minti 14 duk a babban layi na babbar kasuwar.

An shaida ganin gawawaki a zube inda ake kwasar wadan da ke da sauran numfashi zuwa babban asibitin garin Gombe da kuma asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da shi ma ke can Gombe.

Ba wanda ya iya bayyana yadda al’amarin ya auku sai dai wakilinmu ya tattauna da wasu, ga ma abinda wani da abin ya faru kusa da shi ke cewa.