Tagomashin masu kyamar baki a Jamus | Labarai | DW | 01.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tagomashin masu kyamar baki a Jamus

Jam'iyyar masu kyamar baki a Jamus ta samu tagomashi a zabuben 'yan majalisun dokoki a jihohi biyu na gabashin Jamus, da aka gudanar a ranar Lahadi, jam'iyyar ta samu tagomashi fiye da irin wanda ta samu a shekarar 2014.

Jörg Meuthen jagoran jam'iyyar AfD na taya Jörg Urban murnar nasara a zabe

Jörg Meuthen jagoran jam'iyyar AfD na taya Jörg Urban murnar nasara a zabe

A Jihar Saxony jam'iyyar CDU ce ke kan gaba da kaso 32, cikin dari, a yayin da jam'iyyar masu akidar kyamar baki ta samu kaso 27,5 cikin dari.

Haka kuma a jihar Brandenburg jam'iyyar SPD ta samu kaso 27,5 a gaban CDU,  a yayin da ita kuwa  AfD ta samu fiye da kaso 22.

A karshen watan Oktoban wannan shekarar ne, za a sake gudanar da zaben 'yan majalisun dokoki a wata jihar da ke gabashin na tarayyar Jamus