Tafiye-tafiyen Shugaba Buhari na jan hankali | BATUTUWA | DW | 03.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Tafiye-tafiyen Shugaba Buhari na jan hankali

Kasa da watanni bakwai da darewa kan karagar mulki, mahawara ta barke cikin kasar game da sakarabtu na shugaban kasar da ya karade kasashe hudu a kasa da tsukin makonni biyu

Kama daga Iran zuwa Malta da kasar Faransa sannan kuma yanzu kuma Africa ta kudu dai, cikin kasa da tsawon makonni biyu shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi nasarar karade kasashen duniya har guda hudu. A wani abun da ke zama kafa tarihin zama daya a cikin mafiya kai kawo ga shugabanni na kasar a kalla tun bayan sake komawar demokaradiyyar kasar shekaru 16 da doriya.

To sai dai kuma daga dukkan alamu shugaban da ke cikin watanninsa na bakwai kuma keda alkawarin sauya rayuwa na neman jawo mahawara cikin kasar a bisa alfanun yawon nasa.

Duk da cewar dai a kusan dukkanin guda hudun fadar gwamnatin kasar ta kare da bada hujja ta dalilai dama irin alfanun da kasar take shirin samu a gaba, ga 'yan kasar da dama dai kai kawon na Buhari na zaman alamar kauce wa matsalolin cikin gida tare da komawa ya zuwa karatun ko'in kula a cikin jerin matsaloli.

Har ya zuwa yanzu dai Abujar ta gaza sauke nauyin albashin ma'aikatan da ke mata aiki. Ko bayannan kuma ga mummuna na karancin man fetur din da ke zaman ruwan dare gama duniyar kasar.

Uwa uba sai matsatsi na talaucin da ke dada zurfi a zukata na 'yan kasar kuma babu alamar sauki.

Abun kuma da ya sa 'yan kasar da dama ke kallon da ya dace ga shugaban na zaunawa a Abuja da nufin neman mafitar matsalolin da ke da nisa da kokari na sauya rayuwa ta 'yan kasar a bangare na limaman sauyin.

To sai dai kuma a tunanin Abdul Azeez Yari Abubakar da ke zaman shugaba na kungiyar gwamnoni ta kasar sannan kuma daya a cikin jagororin sauyin, rashin sani na hali na kasa ya sanya guna-guni a tsakanin masu tunanin ba dai dai ba.

Ko bayan kokari na neman mafitar matsalolin gado, ana kuma kallon yar yawon ta Buhari, a matsayin wani yunkuri na jaddada tasirin kasar ta Najerirya a duniya, musamman ma bayan daukarsa zuwa tabo da ake zargin 'yan lemar kasar da yi a shekarun can baya.

Duk da cewar dai ya jima ya na taka rawa a fage na siyasar tarrayar, sabon shugaban da ke watannin farko a gadon mulki, na zaman bako a idanu na duniya da ke bukatar tabbatar da koma wane ne kafin iya kaiwa ga gini na aminci dama aiki da kasar a tunanin Dr Husaini Abdu da ke zaman wani masani kan harkoki na siyasa a kasar.

Abun jira a gani dai na zaman tasirin yar yawon ga 'yan kasar da ke kishirwar sauyi da kuma tuni suka fara nuna alamun gajiya da hali na rashin da yake neman dorewa ga rayuwa bayan zaben sauyin.

Sauti da bidiyo akan labarin