1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta yi kashedi ga Philippines

Abdourahamane Hassane
September 26, 2023

Takaddama tsakanin kasashen biyu ta barke a kan tekun Chinar, wadda ta hana jiragen kasar ta Philipins shiga wasu sasan tekun.

https://p.dw.com/p/4Wq5h
Schiff der chinesischen Küstenwache blockiert das  philippinische Küstenwache
Hoto: Aaron Favila/AP/picture alliance

China ta gargadi kasar Philippines da cewar ta daina wasa da wuta kan abin da ta kira tsokana a tekun kudancin kasar na Chinar. Wanda ya zama wata hanya ta zirga-zirga jiragen ruwa na kasashen yanki, da China ba ta amince su rika ratsawa ba a wani tsibirinta dake kan ruwan tekun. Saboda haka Chinar ta ja wani dogon layi na wani shinge balanbalo domin  hana jiragen ruwan keta tsibirin na Huwangin.To sai dai a makon jiya jami'an da ke gadin gabar teku na Philippines sun cire shingen wanda suka ce yana kawo cikas a kan harkokin zirga-zirga a kan tekun Chainar. A shekara ta 2016,kotun kasa da kasa ta ICC a kan karar da Philippines ta shigar ta yanke hukuncin cewar babu wani dalili na shari'a ga kasar China na neman  'yancin  a kan yawancin wannan teku da albarkatunsa. Sai dai Chinar ta ki ta martaba hukuncin kotun na ICC.