Taba Ka Lashe: Azumi cikin zafi a Najeriya | Zamantakewa | DW | 27.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Taba Ka Lashe: Azumi cikin zafi a Najeriya

A yayin da kwanakin azumin watan Ramadan ke wucewa sannu a hankali, ana ci-gaba da kwalla zafi a yankunan arewacin Najeriya, wanda hakan ke zaman kalubale ga masu ibadar.

To ko baya ga yanayin zafin wani abin da ke ci wa Musulmin tuwo a kwarya shi ne karancin na gwamna masu gidan rana ga kuma matsalar rashin tsaro musamman a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya. A duk shekara dai gwamnati na ba da taimako don saukaka radadin kunci da masu karamin karfi daga cikin masu azumin kan samu kansu a ciki. Yankin arewa maso gabashin Najeriya dai na fama da matsaloli na rashin tsaro, ko a 'yan kwanakin nan ma masu tada kayar baya sun kai hare-hare a wurare dabam-dabam a arewacin Najeriya. Wannan ya kara jefa yanayin azumin musamman irin hada-hada da aka saba yi lokacin azumi cikin rashin tabbas. Bugo da kari bayan wannan matsala ga kuma matsaloli na rashin kudi a hannun jama'a

Sauti da bidiyo akan labarin