Taba Ka Lashe: 23.08.2017
August 28, 2017Talla
A kwanakin baya ne a gun wani taro da suka yi a garin Gombe da ke arewacin Najeriya, shehunan Malamai daga kasashen nahiyar Afirka suka nemi gwamnatoci a dukkanin matakai da su dauki matakai na gyara zukatan matasansu zama masu son al'umma, suka ce ta haka ne kawai za a magance cusa wa matasa tsattsauran ra'ayi da ke sanya su cikin kungiyoyin masu gwagwarmaya.