Taba Ka Lashe: 05.04.2017 | Al′adu | DW | 10.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Al'adu

Taba Ka Lashe: 05.04.2017

Kokarin magance rikice rikice tsaknin mabiya addinai mabanbanta a Najeriya.

A Najeriya wata matsala da ta dade ta na ciwa mahukunta da shugabannin addini tuwo a kwarya ita ce ta rikice rikicen da ake samu a tsakanin mabiya addinai mabanbanta, matsalar da a wasu lokutan kan kai ga hasarar rayuka.

A kan haka ne wasu kungiyoyin addinan na Kirista da musulmi a kaduna suka hada kai wajen jawo hankalin matasa domin su kaunaci juna tare da karfafa cudanya da kyakkyawar zamantakewa tsakanin musulmi da Kirista.

To ko menene shugabannin suka lura da shi a yanzu, ya sa su daukar wannan mataki na kyautata zamantakewa tsakanin musulmin da Kirista musamman a tsakanin dalibai? Sai a saurari shirin domin jin karin bayani.

Sauti da bidiyo akan labarin