Taba Ka Lashe: 02.08.2017
August 6, 2017Talla
Wata tawagar manyan malaman Jami’o’in masana tarihi da al'adu daga kasashen Jamus da Ingila da Rasha da kuma Amirka sun hallara a cibiyar tattara kayayyakin tarihin arewacin Najeriya da ke a Kaduna inda suka gana da malaman jami’o’in Najeriya da zumar koya wa malaman jami’o’in Najeriya yadda ake alkinta kayayyakin tarihi musanman ma dai na rubuce-rubuce kamar ajami da Hausa, da Kanuri da wasu harsunan Najeriya.