Sulhu a rikicin siyasar Burkina Faso | Labarai | DW | 21.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sulhu a rikicin siyasar Burkina Faso

Masu shiga tsakani na kasa da kasa a Burkina Faso sun fitar da wani sabon jadawali da zai bayar da damar mayar da kasar kan turbar dimokaradiyya.

Kokarin shawo kan rikicin siyasar Burkina Faso

Kokarin shawo kan rikicin siyasar Burkina Faso

Yayin taron da suka gudanar a wannan Lahadi karkashin jagorancin shugaban kasar Senegal Macky Sall da takwaransa na Jamhuriyar Benin Thomas Boni Yayi sun bukaci da a dawo da shugaban kasar na rikon kwarya da sojojin suka hambarar a makon jiya kana a yi wa sojojin da suka jagorancin juyin mulkin afuwa. Sun kuma bukaci da a baiwa magoya bayan tsohon shugaban kasar da masu zanga-zanga suka tilastawa ajiye mukamin nasa Blaise Compaore damar tsayawa takara a zaben da za a gudanar a watan Oktoba mai zuwa.

A baya dai mahukuntan kasar ta Burkina Faso sun haramtawa duk wani da ke mara wa Compaore baya tsayawa takara a zabukan kasar da aka shirya gudanarwa domin mayar da kasar bisa tafarkin dimokaradiyya bayan kwashe shekaru 27 karkashin jagorancin Compaore.