Sudan za ta mika al-Bashir ga ICC | Labarai | DW | 11.08.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan za ta mika al-Bashir ga ICC

Gwamnatin kasar Sudan ta bayyana aniyarta na mika tsohon shugaban kasar Omar Hassan al-Bashir ga kotun kasa da kasa da ke hukunta masu aikata laifukan yaki wato ICC da ke birnin The Heague na kasar Netherlands.

Gipfeltreffen der Arabischen Liga in Doha Omar Hassan Al Bashir

Omar Hassan al-Bashir ya kawashe shekaru yana mulki kafin kifar da gwamnatinsa

Ministar harkokin kasashen waje ta kasar Sudan din Mariam al-Mahdi ce ta sanar da hakan ga kamfanin dillancin labaran kasar Suna, inda ta ce za su mika al-Bashir da aka kifar da gwamnatinsa a shekara ta 2019 da sauran wadanda kotun ta ICC ke nema zuwa birnin na The Heague. Da ma dai tun a shekara ta 2008 ne kotun ta ICC ta nemi a mika mata al-Bashir din, bisa zarginsa da aikata laifukan yaki a yankin Dafur na kasar ta Sudan.