Sudan ta Kudu na amfani da yara a yaki | Siyasa | DW | 29.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sudan ta Kudu na amfani da yara a yaki

Asusun kula da Kananan Yara na duniya ya bayyana adadin yara da aka tilasta shiga fagen yaki a Sudan ta Kudu. Sai dai UNICEF ya yi nasarar kubutar da wasu daga cikinsu.

Yara da dama ne dai ake tilastasu daukar makamai a kasar Sudan ta kudu, wadanda aka kai ga kubutar da dubu uku daga cikinsu. Wadannan yara sun kasance karkashin bangaren 'yan tawaye. John Budd wanda shi ne kakakin asusun UNICEF a Sudan ta kudu, ya ce "yaran kimanin 260, dukkaninsu maza ne. Akasarinsu sun kasance a hannun 'yan tawayen kusan shekaru hudu. Mafi yawansu sun ga mummunan yaki.

Shekarun yaran da aka kwato 11 ne zuwa 17, wadanda bangaren 'yan tawayen SSDA na Sudan ta kudu suka sa aikin soje ba da son ransu ba. Mista Budd na UNICEF ya ce hukumarsa za ta kula da su yadda ya kamata.

Südsudan Juba Riek Machar Salva Kiir 09.07.2013

Shugaban 'yan tawaye da shugaban Sudan ta Kudu na da hannu a sa yara aiki soji.

Ya ce "Da farko dai za a samar musu wuraren kwana, da abin ci da sha. Za a binciki lafiyarsu, kana a basu duk taimakon da suke bukata na dawo da su cikin hayyacinsu. Kuma bayan mun dauki sunayensu, za mu binciki iyalansu don mayar da su gida.

Tun a watan Disamban 2013 ne rikici ya barke tsakanin gwamnatin Salva Kiir da magoya bayan tsohon mataimakinsa Riek Machar. Ko da yake an samu kubutar da yara dubu uku, amma fa akwai sauran dubban yara da ke fagen daga a yakin kasar Sudan ta kudu, a cewar mista Budd na Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya. Ya nunar da cewar "akwai kimanin yara dubu 12 da ake amfani da su a matsayin sojoji. Dakarun gwamnati sun yi alkawarin rage yawan yaran da ke yaki a hannunsu. Muna fatan su ma 'yan tawaye za su yi hakan."

Lafawar rikici tsakanin Salva Kiir da Riek Machar ne zai bayar da tabbacin sako yara da ke fagen daga a Sudan ta Kudu.

Sauti da bidiyo akan labarin