1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya sun kammala aikinsu a Darfur

Abdourahamane Hassane MNA
January 4, 2021

Majalisar Dinkin Duniyar ta kaddamar da shiri janye dakarun a kan bukatar gwamnatin wucin gadi ta Sudan sakamakon cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnati da 'yan tawaye a farkon watan Oktoba.

https://p.dw.com/p/3nUxP
Sudan | UNAMID Mission
Hoto: AFP

A shekara ta 2007 Majalisar Dinkin Duniya tare a hadin gwiwar kungiyar tarrayar Afirka wato AU, suka girke dakaru dubu takwas a yankin Darfur daf da lokacin da yaki ya yi kamari a shekara ta 2003 tsakanin 'yan tawaye da gwamnati, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla dubu 300 kana ya tilasta wa wasu miliyan biyu da rabi ficewa daga matsugunansu. Musa Adam na zaune a cikin sansanin 'yan gudun hijira a kudancin Darfur ya kuma bayyana yakin da ya wakana a matsayin wani mummunan lamari.

"Kisan kare dangi ne baki daya, aka yi  fyade na mata da 'yan mata da ma wadanda shekarunsu ba su kai ba, da duk wani abin ban tsoro da ka sani suka wakana a cikin sansanin 'yan gudun hijirar. Mun ga yadda mayakan suka rika yin fyade a kan mata tare da bin kauyuka a kan rakuma suna konasu.''

Firamintsan Sudan Abdalla Hamdok ya kuduri aniyar kawo karshen rikicin yankin Darfur
Firamintsan Sudan Abdalla Hamdok ya kuduri aniyar kawo karshen rikicin yankin DarfurHoto: Hannibal Hanschke/Reuters

A 2003 yakin ya barke a Darfur da ke yammacin Sudan, gaba daya yakin ya daidaita kasar, ga kuma fari saboda rashin ruwan sama abin da ya janyo tashin hankali tsakanin makiyaya Larabawa da bakaken fata da ke zaune a yankin. Gwamnati dai ta rika goyon bayan farar fata ta hanyar mayakan sa-kai na Janjawid, hakan ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi na jama'a.

Karin bayani: Darfur: Mutum 9 sun mutu a sakamakon tashin hankali

A shekara ta 2009 zuwa 2010 kotun kasa da kasa da ke birnin The Hague ta ba da umarnin kama Shugaba Omar al-Bashir. Bayan faduwar gwamnatinsa a shekara ta 2019 sabon firaministan kasar Abdalla Hamdok ya kai ziyara a yankin Darfur inda ya yi jawabi ga jama'a.

"Mu kiyaye zaman lafiya a Darfur, mun saurari jawaban wakilanku, ina mai tabbatar muku da cewar gwamnatin wucin gadi za ta kula da kokenku.''

Watanni uku ke nan da suka gabata da gwamnatin wucin gadin ta Sudan da kungiyoyin mayakan da dama har da na Darfur suka saka hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya. Majalisar Dinkin Duniyar dai ta yanke shawarar cewa ba za ta kara tsawaita wa'adin rundunar ba saboda an samu zaman lafiya. Sai dai wa'adin rundunar na zuwa ne a dadai lokacin da ake samun karuwar tashin hankali tsakanin kabilu a yankin na Darfur, wanda a makon da ya gabata mutane 15 suka mutu kana wasu da dama suka jikkata.