1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnati da kungiyoyin 'yan tawayen Sudan sun rattaba hannu

Abdoulaye Mamane Amadou
August 30, 2020

Gwamnatin Sudan da kungiyoyin 'yan tawayen sun yi na'am da rattaba hannu a matakin farko kan wata yarjejeniyar tsagaita wuta a gabanin yin gagarumin bikin sulhu a Juba na kasar Sudan Ta Kudu.

https://p.dw.com/p/3hmYI
sudanesischer Premierminister Abdalla Hamdok
Hoto: picture-alliance/AA/M. Hjaj

An bayyana cewa Firaminista Abdallah Hamdok na Sudan da wasu mukrabban gwamnatin rikon kwarya suka isa a birnin Juba, inda suka gana da shugaba Salva Kiir na Sudan Ta Kudu, kafin ranar Litinin inda daukacinsu da sauran jiga-jigan kungiyar FRS ta 'yan yakin sunkurun kudancin Sudan za su halarci bikin rattaba hannu da gwamnati.

Wannan dai na a matsayin wata matattakalar wanzar da zaman lafiya tsakanin 'yan kasar Sudan a cewar  Firaminista Hamdok.