1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

RSF ta karya yarjejeniyar sulhu a Sudan

Mahmud Yaya Azare LMJ
November 26, 2025

Mayakan RSF a Sudan, ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta watanni uku da ta amince don radin kanta, lamarin da ke mayar da hanun agogo baya, a kokarin lalubo bakin zaren warware rikicin kasar na sama da shekaru biyu.

https://p.dw.com/p/54JrQ
Sudan | Yaki | Gwamnati | Abdul Fattah Al-Burhan | RSF | Mohamed Hamdan Dagalo
Shugaban Sudan Abdul Fattah Al-Burhan da na mayakan RSF Mohamed Hamdan DagaloHoto: Bandar Algaloud/Mahmoud Hjaj/AA/picture alliance

Rahotanni daga gundumar Jabal Moyah ta yankin Kurdafan na tabbatar da cewa, mayakan na RSF sun kaddamar da hare hare a yankin tare da kwace iko da kauyuka, lamarin da ya janyo asarar rayuka da tserewar dubban mutane. Haka kuma mayakan na RSF sun kaddamar da wasu hare-haren da jiraga marasa matuka, kan sansananin sojin gwamnatin Sudan da ke yankin Marwah na jihar Aljazeerah.

Amurka na son kawo karshen yakin Sudan

Hakan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da Mayakan RSF din sukai gaban kansu, wajen shelanta amincewarsu da fara yin aiki da  yarjejeniyar tsagaita wuta ta watanni uku da Amurka ta gabatar, domin bayar da damar shigar da kayan agaji, yarjejeniyar kuma da dakarun gwamnati suka ki amincewa da ita.

Sudan | 2025 | Al-Faschir | Yakin Basasa | RSF | Gwamnati
Al'ummar Sudan na cikin halin tasku sakamakon yakin basasar kasarHoto: Muhnnad Adam/AP Photo/dpa/picture alliance

Dama dai rundunar sojin Sudan ta ce, ba za tai aiki da wannan yarjejeniyar da Amurka tare da kawayenta uku da suka hada kawancen kwar hudu ya kunshi kasashen Masar da Saudiya da Hadadiyar Daular Larabawa, domin kawo zaman lafiya a Sudan din ba, inda shugaban rundunar sojin Sudan din Janar Abdel Fattah al-Burhan ke cewa, daftarin yarjejeniyar shi ne mafi muni a tarihi.

Taka tsan-tsan wajen taimakon gwamnati

A hannu guda, masharhanta na danganta yadda kungiyar tsohon shugaban kasar Omar Hassan Ahmad al-Bashir da yin kaka gida cikin rundunar sojin Sudan da ke taya al-Burhan fada, lamarin da ya sanya kawancen na kwar hudu ke taka tsan-tsan wajen tallafawa gwamnati ta murkushe 'yan tawayen na RSF.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani