1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sudan: Hare-hare uku sun wakana a cibiyoyin lafiya

Mouhamadou Awal Balarabe
February 8, 2026

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce sama da mutane 30 sun mutu a mako guda a yankin Kordofan ta Kudu na Sudan, a jerin hare-hare da aka kai kan cibiyoyin kiwon lafiya a yankin da ke fama da karancin abinci mai gina jiki.

https://p.dw.com/p/58JLZ
Hoto: El Tayeb Siddig/REUTERS

Cikin wata sanarwar da shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ya wallafa a shafin X, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce Kordofan ta kudu ya zama muhimmin fagen daga a yakin da ake yi tsakanin dakarun gwamnatin Sudan da na rundunar ko ta kwana ta RSF tun daga watan Afrilun 2023.

Amma Darakta Janar na WHO ya kara da cewar akwai bukatar "duniya baki daya ta goyi bayan shirin zaman lafiya a Sudan da nufin kawo karshen tashin hankali, da kare jama'a da kuma sake farfado da tsarin kiwon lafiya."

Karin bayani: Sudan: Za a kawo karshen yakin basasa?

Rikicin da ya barke a yankin Kordofan ya tilasta wa dubban mutane shiga cikin hali na 'yunwa, sannan ya tilasta wa mutane 88,000 tserewa daga matsugunansu tsakanin Oktoba da Janairu, a cewar alkaluman Majalisar Dinkin Duniya.

Yakin Sudan dai, ya kashe dubban mutane, tare da raba kimanin mutane miliyan 11 da muhallansu a kasar, lamarin da ya haifar da abin da Majalisar Dinkin Duniya ta kira "mafi munin matsalar ayyukan jin kai a duniya."