Sudan: Firaiminista Abdallah Hamdok ya ziyarci Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 12.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan: Firaiminista Abdallah Hamdok ya ziyarci Sudan ta Kudu

Firaiministan Sudan Abdallah Hamdok ya kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu kasar Sudan ta Kudu don kammala tattaunawar sulhu tsakanin 'yan tawaye da gwamnati.

Firaiminista Hamdok tsohon wakilin Majalisar Dinkin Duniya, ya amshi rantsuwar kama aiki karkashin jarjejeniya tsakanin rundunar sojin Sudan da kungiyoyin fararen hula masu fafutukar kafa dimukuradiyya a Sudan din bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir.

Sabuwar majalisar gwamnatin hadaka a Sudan ta kudiri aniyar kawo karshen ayyukan ta'addancin da suka addabi kasar karkashin mulkin tsohon shugaba al-Bashir, da kuma kawo karshen rikicin tsaknin 'yan tawaye da mahukunta a Sudan ta Kudu.

Batun kasuwanci da inganta alaka da kuma harkokin mai na daga cikin batutuwan da jagororin kasashen biyu za su tattauna.