1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soke wasu kungiyoyin farar hula a Najeriya

Uwais Abubakar Idris AH
April 6, 2018

Gwamnatin Najeriya na zargin wasu kungiyoyin da karya ka'ida bisa zargin wawure kudade da daukar nauyin ayyukan ta’addanci.

https://p.dw.com/p/2vdF6
Nigeria - Jugenddemonstration "not too young" in Abuja
Hoto: Uwais Abubakar Idris

Wannan sabon tsarin sanya idanu a kan kungiyoyin farar hula da ke kare dimokuradiyya da hakkin dan Adam da ma yaki da cin hanci da rashawa da gwamnati ta fara a karkashin hukumar kula da  binciken kwakwaf a kan harkokin kudi ta Najeriyar, tsari ne da aka bayyana shi da wanda zai sa ido a kan harkokin kungiyoyi da nufin gano wadanda suka aikata ba dai dai ba.

Mr. Francis Usani darakta ne a hukumar kula da binciken kwakwaf a harkokin kudaden Najeriya da ya nuna cewa:

"Mun yi haka ne domin samun dorewar ayyuka, sannan muna yin haka ne da nufin wayar da kan kungiyoyin domin mun lura akwai bukatar yin haka."

Nigeria Abuja Proteste Regierung
Wasu kungiyoyin farar hula a NajeriyaHoto: DW/U. Musa

To sai dai tuni kungiyoyin farar hula da suka taimaka rushe wancan yunkuri da aka yi a majalisa suka bayyana adawa da shirin, kan cewa wata dabara ce ta bullo da wannan doka ta wata hanya. 

Duk da dalilai da gwamnatin ta bayar na samar da dokar, ana kallon kungiyoyin a matsayin wadanda ke taimakawa wajen bunkasa dimokradiyya da suke zama masu ikon fadin gaskiya komin dacinta ga mahukuntan Najeriya. Abin da ya sanya Auwal Musa Rafsanjani na kungiyar Cisilac bayyana cewa.

"Akwai hatsarin rasa kungiyoyj da za su fadi gaskiya, tun da yanzu shugabannin jama'a da shugabannin addinai ba su iya fadawa gwamnati gaskiya a kan yadda za a tafi da jagorancin kasa."

Abin jira a gani shi ne ko wannan karon abin zai yi tasiri a kokarin sa ido a kan kungiyoyin. A watannin baya ta kai ga gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa za ta sa ido a kan ayyukan kungiyoyin a jihar don sanin ayyukan da suke yi.