Sojojin Turkiya sun samu mafaka a Girka | Labarai | DW | 27.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Turkiya sun samu mafaka a Girka

Sojojin Turkiya takwas da suka tsere zuwa Girka bayan yunkurin juyin mulki sun samu wata dama ta zama zuwa lokacin da za a tantance takardun da suka mika.

Sojojin Turkiya takwas da suka tsere daga kasar lokacin yunkurin juyin mulki, sun samu karin dama ta zama a kasar Girka zuwa lokacin da za a tantance takardunsu na neman mafaka. Wani lauya da yake wakilatan mutanen ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa hukumomin Girka sun amince da bukatar saboda rayuwar sojojin na cikin barazana bisa matakan da gwamnatin Turkiya take dauka tun bayan yunkurin juyin mulkin na ranar 15 ga wannan wata na Yuli.

Sojojin takwas na kasar ta Turkiya sun tsere zuwa kasar ta Girka cikin karamin jirgin sama jim kadan bayan yunkurin kafar da gwamnatin ta Turkiya ya ci tura. Tun farko wata kotun kasar ta Girka ta yi wa mutanen takwas daurin jeka ka gyara halin ka, na tsawon watanni biyu saboda shiga kasar ta hanyoyin da suka saba ka'ida.