Sojojin Turkiya sun kai hari kan ′yan awaren Kurdawa | Labarai | DW | 07.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Turkiya sun kai hari kan 'yan awaren Kurdawa

Kasar Turkiya ta mayar da martani bayan hallaka mata sojoji 15 ta hanyar harin kwanton bauna na 'yan awaren Kurdawa.

Sojojin Turkiya sun kaddamar da farmaki da sanyin safiyar wannan Litinin kan sansanoni 13 na 'yan awaren Kurdawa, kwana guda bayan harin bam da ya hallaka sojoji 15 yayin da wasu da dama suka samu raunika.

Jim kadan bayan harin na 'yan aware Firaminista Ahmet Davutoglu ya katse kallon kwallo domin gudanar da taron gaggawa, inda daga bisani aka tura jiragen saman yaki biyu da suka mayar da martani. 'Yan awaren na Kurdawa sun dade suna takun saka da gwamnatin kasar ta Turkiya.