Sojojin Sudan 9 sun mutu | Labarai | DW | 28.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Sudan 9 sun mutu

Wani janar tare da wasu jami'an soji tara a Sudan, sun gamu da ajalinsu a wani harin kwantan baunar da 'yan tawaye suka yi masu a yankin Darfur.

Bayanai dai sun ce sabon rikici neya barke a kudancin yankin na Darfur, bayan wani yunkurin da sojoji suka yi na kwace makamai daga hannun mayakan tarzoma. Ministan tsaron kasar ta Sudan Ali Mohammad Salim, ya ce sun kama wani zarton 'yan tawayen yankin Musa Hilal, lamarin da ya kaiga kwantar da kurar rikicin.

Yankin na Darfur dai ya shiga rikici ne a shekarar 2003, lokacin da galibin bakar fata suka dauki makamai don yaki da gwamnatin da larabawa ke jagoranta, koda yake gwamnatin ta sanar da tsagaita buda wuta a bara.