1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Nijar sun kashe 'yan ta'adda fiye da 100

February 22, 2020

Dakarun kasar Nijar tare da hadin gwiwar na Faransa sun yi nasarar kashe 'yan ta'adda 120 a yankin Tillaberi mai iyaka da Mali da kuma Burkina Faso.

https://p.dw.com/p/3YB0l
Niamey Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Petesch

Ma'aikatar harkokin tsaron Jamhuriyar ta Nijar, ta ce baya ga kisan 'yan bindigar, mayakan sun kwace wata naurar hada bama-bamai.

Hukumomin sun ce babu asarar rai daga bangaren sojin kasar da ma na Faransar, tare da yaba nasarar da suka samu ta hanyar hada karfin.

Dama dai an karfafa tsaro a yankin na Tillaberi, tare da dakatar da amfini da babura, bayan hare-haren watan Disambar bara, da suka yi sanadiyyar mutuwar sojin kasar 174.

Akwai ma dokar ta-baci da ke ci a yankin yau shekaru biyu ke nan.

Kasar Faransa ta yi alkawarin kara yawan dakarunta a bana, a tsakanin wasu kasashen yammacin Afirka da ke fama da fitintinu, da kimanin 600 kan wasu dubu 4,500 da dama ke baje a kasashen.