Sojojin Najeriya sun sake kwato mata da kananan yara | Labarai | DW | 06.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Najeriya sun sake kwato mata da kananan yara

Rundunar sojan Najeriya ta sanar a wannan Laraba cewa, ta sake kwato wasu mata da kananan yara a kalla 25 da 'yan Boko Haram suka yi garkuwa da su a dajin Sambisa.

Rundunar ta ce sojojinta sun hallaka mayakan na Boko Haram da suka yi garkuwa da wadannan mutane. Sanarwar ta ce a kalla sun lalata sabin sansanoni guda bakwai na 'yan kungiyar a jiya Talata, kuma sun hallaka mayakan masu yawan gaske a kokarin da sojojin na Najeriya ke yi na fitar da su daga dajin na Sambisa.

Da ma dai rundunar sojan na Najeriya ta sanar a baya cewa ta samu kwato fiye da mutane 700 da suka hada da mata da kananan yara da aka yi garkuwa da su a sansanoni da dama da 'yan kungiyar ta Boko Haram a dajin na Sambisa da ke cikin jihar Borno, inda a halin yanzu a kalla mata da yara 275 ne ke samun kulawa a sansanonin asibitocin garin Yola na jihar Adamawa domin kula da su.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba