Sojojin Najeriya na samun galiba a kan Boko Haram | Labarai | DW | 01.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Najeriya na samun galiba a kan Boko Haram

Sojojin Najeriya sun yi ikirarin sake kwace garin Gamboru Ngala daga hannun tsagrun Boko Haram masu dauke da makamai

Sojojin Najeriya sun bayyana samun galiba kan kungiyar Boko Haram inda suka sake kwato garin Gamboru Ngala na Jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar wanda yake makwabtaka da kasar Kameru.

Wani kakakin soji na kasar ya fitar da sanarwar da ke cewa a wannan Talata sojojin suka sake kwace garin daga tsagerun kungiyar Boko Haram. Mahukuntan a Najeriya na ci gaba da daukan matakai magance rikicin na Boko Haram ya kai ga mutuwar dubban mutane.