1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

China na gagarumin atisayen soji kusa da Taiwan

May 23, 2024

China ta bude sabon babin takun saka da sabbin hukumomin Taiwan tare da kaddamar da atisayen sojojin ruwa da na sama da kuma na kasa a kusa da tsibirin da take ikirarin mallakinta ne.

https://p.dw.com/p/4gAg1
Taiwan Hsinchu Mirage-2000-Kampfjets der Luftwaffe
Hoto: YASUYOSHI CHIBA/AFP

China ta kaddamar da wani gagarumin atisayen sojoji a kusa da Taiwan a Alhamis din nan, wanda ta bayyana a matsayin ladabtarwa mai tsanani ga sabon shugaban tsibirin Lai Ching-te lamarin da mahukutan Taiwan din suka kira da takala.

Dama dai a farkon wannan mako Beijing ta yi bazanar hukunta sabon shugaban tsibirin bayan wani jawabin da ya yi a lokacin da yake karbar rantsuwar kama aiki, kalaman da ta siffanta da 'ikirarin kwatar 'yancin kan Taiwan'.

Karin bayani: An rantsar da Ching-te a matsayin shugaban Taiwan

Sai dai a cikin wata sanarwa, ma'aikatar tsaro ta Taiwan ta yi Allah waddai da wannan atisaye tare da sanar da cewa ta tura sojojinta na ruwa da na kasa domin kare 'yanci kai da kuma dimokuradiyya.

China dai na daukar tsibirin Taiwan a matsayin daya daga cikin lardunanta wanda har yanzu ba ta yi nasarar hade shi da sauran yankunan nata ba tun bayan kawo karshen yakin basasar kasar a shekarar 1949.

Karin bayani: Chaina ta jaddada kudirinta na hade Taiwan

A baya-bayan ma mahukuntan China sun ce sun aminta da hade tsibirin mai al'umma miliyan 23 cikin lumana amma sai dai ba su fidda tsammanin yin amfani da karfin soji ba don cimma wannan buri.