1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun yi harbe-harbe a Burkina Faso

January 23, 2022

An ji rugugin muggan makamai a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso da kewaye, inda hankali ya tashi a kasar a kan yiwuwar ko an kifar da gwamnati ne.

https://p.dw.com/p/45yZp
Burkina Faso Ouagadougou  Unruhen
Hoto: picture alliance / ASSOCIATED PRESS

Rahotannin da ke fitowa daga Ouagadougou babban birnin kasar Burkina Faso, na cewa an ji rugugin muggan makamai a birnin da kewaye, inda fargaba ta lullube kasar a kan yiwuwar kifar da gwamnatin Shugaba Roch Marc Christian Kabore.

Da fari dai an yi zaton sojoji ne ke furjanye wa shugabanninsu, inda kafar watsa labaran RTB a kasar, ta siffanta lamarin da rashin gamsuwa daga sojojin Burkina Faso.

Hukumomi dai sun tabbatar da harbe-harebn daga barikin soji da ke a Ouagadouguo, sai dai sun kore batun juyin mulki.

Babu dai labarin kame Shugaba Roch Marc Christian Kabore ya zuwa yanzu, kamar yadda su ma jagororin sojin kasar suka fada.

A ranar Asabar ma 'yan kasar ta Burkina Faso sun yi zanga-zangar neman gwamnati ta kawo karshen rashin tsaro da ake fama ada shi daga hare-haren masu ikirarin jihadi.