1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun tsawaita wa'adin mulkinsu a Burkina Faso

May 26, 2024

Shugaban mulkin sojin kasar Keftin Ibrahim Traore ya ce gwamnatin za ta kwashe watanni 60 tana mulki daga ranar biyu ga watan Yulin bana lokacin da suka tsara ba da ga gwamnatin dimukuradiyya.

https://p.dw.com/p/4gIMo
Keftin Ibrahim Traore, shugaban mulkin soja a Burkina Faso
Keftin Ibrahim Traore, shugaban mulkin soja a Burkina Faso Hoto: Kilaye Bationo/AP/picture alliance

Gwamnatin soji a Burkina Faso, za ta ci gaba da mulki har zuwa wasu shekaru biyar nan gaba, bayan shawarar da mahalarta taron nema wa kasa mafita da aka yi suka bayar.

A shekara ta 2022 ne sojoji suka kifar da gwamnatin dimukuradiyya a Burkina Fason, tare da alkawarin shirya zabe cikin watan Yulin bana, sai dai sun jingine yiwuwar samun hakan da ingantuwar yanayi na tsaro.

Wani sabon daftari da shugaban mulkin sojin kasar Keftin Ibrahim Traore ya sanya wa hannu, ya ce gwamnatin za ta kwashe watanni 60 tana mulki daga ranar biyu ga watan Yulin bana.

Haka ma daftarin ya nuna cewa Keftin Traoren na iya tsayawa takara a lokacin zaben da a yi bayan shekarun biyar.

Kasar ta Burkina Faso dai ta sha fama da hare-haren ta'addanci a bara da suka yi sanadin mutuwar sama da mutum dubu takwas.