Sojoji Najeriya sun fatattaki ′yan Boko Haram | Labarai | DW | 12.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojoji Najeriya sun fatattaki 'yan Boko Haram

Sojojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram a garin Konduga

A wannan Jumma'a rundunar sojin Najeriya ta bayyana samun nasarar dakile harin da tsagerun kungiyar Boko Haram masu dauke da nmakamai suka kai garin Konduga mai kisan kilo-mita 35 daga Maiduguri fadar gwamnatin Jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar.

A cikin wata sanarwa wani kakakin soji ya ce yayin fafatawar an hallaka 'yan Boko Haram masu dauke da makamai fiye da 100, da motocin da tsagerun suka yi amfani da su wajen kai harin. Tun farkon wannan makon kungiyar dattawa ta Jihar Borno ta nemi gwamnatin kasar ta tsaurara matakan tsaro ganin yadda 'yan bindiga na Boko Haram ke yin tsinke wa birnin na Maiduguri.

Yanzu haka 'yan kungiyar ta Boko Haram suna rike da wasu garuruwa da ke yankin arewa maso gabashin kasar ta Najeriya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba