Sojin Siriya sun tsagaita wuta | Labarai | DW | 06.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojin Siriya sun tsagaita wuta

Hukumomin sojin Siriya sun sanar da daukar matakin tsagaita wuta na tsawon kwanaki uku a duk fadin kasar daga bakin karfe goma agogon GMT na daren ranar Talata.

Sun sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da suka fitar a wannan Laraba wacce kuma kafofin yada labarai na gwamnatin kasar suka yada.

Sai dai sanarwar wacce ta zo a daidai loakcin da ake gudanar da bukukuwan Sallah karama a kasar ba ta yi karin haske ba a kan ko matakin tsagaita wutar zai shafi Kungiyar IS da ta Al-Nusra.

Sai dai kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP da ma kuma kungiyoyin sa ido sun ruwaito cewa duk da wannan sanarwa ta tsagaita wuta, unguwannin gabashin birnin Aleppo sun fuskanci hare-haren makaman atilare a wannan Laraba inda aka samu mutuwar mutun daya a yayin da wasu da dama suka jikkata lokacin da wani makami ya fada a kusa da wani filin Sallar idi.