Sojin Nijar da na Najeriya sun kashe ′yan Boko Haram | Labarai | DW | 04.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojin Nijar da na Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram

Sojojin Nijar da na Najeriya na rundunar yaki da Boko Haram a yankin tafkin Chadi sun halaka mayakan Boko Haram 53 a wani farmaki kan iyaka da Najeriya.

Sojojin Nijar da takwarorinsu na Najeriya na rundunar hadin gwiwa da ke yaki da Boko Haram a yankin tafkin Chadi, sun yi nasarar halaka mayakan Boko Haram 53 a cikin wani farmakin kasa da na sama da suka kaddamar a ranar Lahadi da ta gabata a wasu wuraren buyar mayakan na Boko Haram a yankin tafkin na Chadi kan iyaka da Najeriya. 

Ofishin ministan tsaron kasar ta Nijar ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya inda ya ce sojojin kasashen biyu sun kuma yi nasarar lalata motoci hudu na kungiyar ta Boko Haram da suka hada da daya mai sulke, da kuma karbo tarin makamai da kwayoyin sa maye. 

Sanarwa ofishin ministan tsaron kasar ta Nijar ta ce babu asarar rai ko daya daga bangaren sojojin kasar ta Nijar wadanda amma uku sun jikkata a cikinsu. Ta kara da cewa yanzu haka sojojin kasar biyu na ci gaba da farautar mayakan na Boko Haram da suka tarwatsa daga sansanoninsu. 

Wannan na zuwa ne kwana daya bayan da gwamnatin kasar ta Nijar ta sanar da dakile wasu jerin hare-haren ta'addanci da Boko Haram ta yi yinkurin kaiwa a biranen Diffa da Yamai a ranar Lahadi da ta gabata.