Sojin Najeriya sun kashe ′yan Boko Haram | Labarai | DW | 23.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram

Sojojin Najeriya sun yi ikrarin kashe gwamman 'yayan kungiyar Boko Haram tare da ceto wasu mutane 20 a dajin Sambisa da ke jihar Borno.

A Najeriya sojojin gwamnatin kasar sun yi ikrarin hallaka gwomman mayakan kungiyar Boko Haram lokacin wani hari da suka ce sun kaddamar a jiya juma'ar a sansanin 'yan kungiyar da ke cikin dajin Sambisa na Arewa maso gabashin kasar.

Haka zalika sojojin Najeriyar sun ce sun yi nasarar kwato wasu mutane 20 akasarinsu mata da yara kanana wadanda 'yan Boko Haram din suka yi garkuwa da su.Sai dai rundunar sojin Najeriyar ta ce ta yi asarar sojinta daya kuma wasu goma sun ji rauni a cikin fafatawar ta jiya.

Sai dai har kawo yanzu babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wadannan alkalumma da sojojin Nijeriyar su ka bayyana. A makwanni baya bayannan dai nasarori da dama ne sojin Najeriyar suka yi a cikin fadansu da kungiyar ta Boko Haram inda su ka ceto sama da mutane 700 daga hannun 'yan kungiyar ta Boko Haram