1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi wa sojin Najeriya kaunatar bauna

Abdullahi Tanko Bala
October 4, 2019

A Najeriya wani harin kwantar bauna na yan bindiga a kauyan Sinke a karamar hukumar Anka dake jihar Zamfara areawa maso yammacin kasar ya halaka Sojojin Nigeria 9 da 'Yan sanda uku. 

https://p.dw.com/p/3Ql0w
Nigeria - Boko Haram Konflikt
Hoto: picture alliance/dpa

Wani mazaunin yankin wanda bai so a ambacin sunansa ba ya shaida wa wakilinmu Yusuf Ibrahim Jargaba cewa maharan sun yi wa sojojin kwantar bauna inda suka bude masu wuta 

Wani Jami'in sojan mai mukamim Kanal da bai so a ambaci sunansa ba ya tabbatar da afkuwar lamarin inda yace nan gaba za su yi magana da manema labaru. 

A baya dai yan bindigar sun sha kashe al'umma a jihar ta Zamfara a yanzu kuma suka sake salo zuwa ga jami'an tsaro.