Sojin Birtaniya na binciken zargin cin zarafin wasu matasan Iraki | Labarai | DW | 12.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojin Birtaniya na binciken zargin cin zarafin wasu matasan Iraki

Gwamnatin Birtaniya ta ba da umarnin yin binciken zargin da aka yi wa sojojin kasar na cin zarafin wasu matasan Iraqi. Hakan dai ya biyo bayan wani faifayen bidiyo ne da tashoshin telebijin da dama suka nuna wanda a ciki sojojin Birtaniya ke shuri tare da dukar matasan na Iraqi da kulake. Jaridar News Of The world, wadda ta samo faifayen bidiyo din ta ce an dauki faifayen ne shekaru biyu da suka wuce a birnin Basra dake kudancin Iraqi. A lokacin da yake yin Allah wadai da wannan aika-aika sakataren kudin Birtaniya Gordon Brown ya ce za´a gurfanad da wadanda aka same su nda hannu a wannan al´amari gaban shari´a.

„Wannan halin ba abin karbuwa ba ne. Tuni dai ma´aikatar tsaro ta ce zata gudanar da cikakken binciken akan wannan zargi. Kuma duk wanda aka samu da hannu za´a yi masa shari´a. Wadanda zasu fi jin takaicin wannan abu su ne sojojin mu masu biyayya wadanda ke aiki tsakani da Allah a cikin kasar Iraqi.“