Sojan Kamaru sun kashe mayakan Boko Haram 40 | Labarai | DW | 02.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojan Kamaru sun kashe mayakan Boko Haram 40

An tafka wata musayar wuta tsakanin sojojin Jamhuriyar Kamaru da mambobin kungiyar Boko Haram ta Najeriya

Jamian tsaro a Jamhuriyar Kamaru sun bayyana cewa sun kashe a kalla mayakan kungiyar Boko Haram 40, wadanda suka kutsa kasar daga Najeriya ta yankin arewa mai nisa.

Bayan wani harin roka kan sojojin na Kamaru da ke yankin Fotokol da mayakan na Boko Haram suka kai, mai magana yawun sojan na Kamaru ya bayyana cewa mayakan sakan na kungiyar Boko Haram sun ja da baya zuwa Najeriya bayan wani gumurzun da suka tafka.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu