Sojan Kamaru sun kashe fiye da ′yan Boko Haram 100 | Labarai | DW | 09.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojan Kamaru sun kashe fiye da 'yan Boko Haram 100

Fafatawa tsakanin dakarun sojan Kamaru da 'yan Boko Haram na ci gaba tsamari inda a bangaren dakarun Najeriya ma ke kara himma wajen sake kwato yankunan da kungiyar ta mamaye.

Mahukunta a kasar Kamaru sun bayyana cewa dakarun sojansu sun kashe fiye da mayakan sakai daga kungiyar Boko Haram 100 bayan wani sumame da kungiyar ta kawo musu adaidai lokacin da dubban jama'a a kan iyakar kasar da Najeriya ke kauracewa muhallansu saboda mamayar kungiyar.

A daren jiya ma dai an gwanza fada tsakanin dakarun sojan na Najeriya da 'yan Boko Haram, a nan ne ma dai Laftanal Adebayo Obasanjo da ga tsohon shugaban Najeriya ya sami rauni.

A cewar mai magana da yawun gwamnatin kasar ta Kamaru Issa Tchiroma Bakary da ya ke jawabi ta kafar gidan rediyo a kasar dakarun sojan na Kamaru sun yi babbar illa ga Kungiyar ta Boko Haram a fafatawar da su ka yi da su a ranar Asanbar a arewacin na Kamaru.

Sai dai wasu rahotanni da ba a tabbatar da sahihancinsuba na cewa Kungiyar ta Boko Haram ta harba bama-bamai a garin Fotokol da ke arewacin na Kamaru kan iyaka da Najeriya.

Babu dai wasu dakaru da aka bayyana cewa sun rasa rayukansu daga bangaren na sojan Kamaru.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu