Siyasar Najeriya ta ja hankalin jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 15.02.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Siyasar Najeriya ta ja hankalin jaridun Jamus

An fi mayar da hankali kan ribar da za a samu domin a Najeriya siyasa ta zama wata harkar kasuwanci inda ake zuba jari ciki domin samun riba a cewar jaridar Süddeutsche Zeitung.

A sharhin jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka za mu fara ne da jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta yi sharhi kan babban zaben da za a gudanar a Najeriya. Jaridar ta ce zabe zai fi zafi ne tsakanin ‘yan takarar manyan jam’iyyun kasar guda biyu, wato Muhammadu Buhari na APC da Atiku Abubakar na PDP. Sai dai duk kanwar ja ce domin ba wanda ya gabatar da wani muhimmin batu ga masu zabe. An fi mayar da hankali kan ribar da za a samu domin a Najeriya siyasa ta zama wata harkar kasuwanci inda ake zuba jari ciki domin samun riba. Jaridar ta ce shekaru 20 ke nan da kawo karshen mulkin soja a Najeriya amma babu wani sauyi na a zo a gani na shugabancin siyasa, inda kulla sabon kawance da sauyin sheka daga wata jam’iyya zuwa wata jam’iyya ya zama ruwan dare.


Vor Wahlen in Nigeria Muhamadu Buhari (M), Präsident von Nigeria, und Atiku Abubakar (r) (picture-alliance/AP/B. Curtis)

Siyasa dai ta zamo hanyar samun kudin cikin sauri a Najeriya

Batun kaura shi ne abin da jaridar Die Tageszeitung ta yi sharhi a kai tana mai cewa a taron kolin da suka yi a farkon mako, shugabannin kasashen Kungiyar Tarayyar Afirka sun nuna goyon bayansu na mayar da yin kaura a matsayin abin da aka saba, wato kaura ba barazana ba ce ta tsaro abu ne da ke bukatar a yi masa hange na ci-gaba. Jaridar ta ce matsayin da Afirka ta dauka kan batun na kaura na zaman hannunka mai sanda ga kasashen Turai da su canja tunaninsu. Sai dai a cewar jaridar wasu shugabannin Afirka ne musabbabin kaurar da al’ummominsu ke yi saboda rashin shugabanci na gari. Zai yi kyau idan bangarorin biyu wato Turai da Afirka suka yi magana da murya guda a kan batun na kaura, domin Turai ma na da nata laifin dangane da halin da Afirka ke ciki. Koma baya na yawan al’umma da karuwar yawan tsofaffi a Turai da bunkasar al’umma babu kakkautawa a Afirka kalubale ne na bai-daya da za a iya magance shi tare.

Migranten vor Libyen (picture-alliance/dpa)

Akwai dai dubban 'yan gudun hijira zuwa Turai daga Afirka


Taron koli na kasuwanci da ya gudana a birnin Accra na kasar Ghana tsakanin kasashen Afirka da Tarayyar Jamus ya dauki hankalin jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung. Jaridar ta ce gwamnatin Jamus ta dauki alkawarin karin tallafi ga matsakaitan kamfanonin Jamus da ke duba yiwuwar zuba jari a Afirka. Jamus dai ta farga cewa yawan kamfanonin kasar da ke aiki a Afirka bai taka kara karya ba duk da bunkasar tattalin arziki na kimanin kashi bakwai cikin dari da ake samu a kasashe irinsu Ghana da Habasha da Cote d’Ivoire. Daga cikin kamfonin Jamus dubu 300 da ke aiki a ketare dubu daya ne kacal ke a Afirka. A kasar Ghana ga misali, inda a ranar Talata aka kammala taron kolin kamfanoni Jamus 80 ne kadai ke a kasar.