Siyasar Burkina Faso da Ebola sun ja hankalin jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 09.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Siyasar Burkina Faso da Ebola sun ja hankalin jaridun Jamus

Duniya ta sanya ido ta ga ko shugabanin rikon kwaryar sojin Burkin Faso, za su cika alkawarin da suka yi na ganin farin hula ya jagoranci iko kafin zaben 2015

A jaridun na Jamus na wannan makon dai dambarwar siyasar Burkina Faso da kuma yakin da ake yi da cutar Ebola ne suka fi daukar hankali, inda a Jaridar Neues Deutschland ta ba da labarin yadda bayan murabus din shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore, kasarta amince da gwamnatin rikon kwaryarda za ta jagoranci kasar zuwa zabukan da ta ke sa ran yi a watan Nuwamban shekara ta 2015 idan Allah ya kai mu.

Kan gaba a taswirar hanyarda mahukuntan rikon suka samar yanzu sun hada da mayar da kundin tsarin mulki da kuma dora farin hula a mukamin shugabanci na riko kafin zaben. Jaridar ta ce a yanzu haka dai Isaac Zida wanda a baya ya kasance na biyu a rundunar fadar shugaban kasa ne ke jagoranci kuma tuni ya gana da 'yan adawa da duk bangarorin da ke da karfin fada a ji a kasar, amma duk da cewa ya ce za a baiwa farin hula riko, har yanzu bai ba da lokaci ko kuma yadda wannan zai faru ba.

Burkina Faso Oppositionspolitikerin Saran Sereme

Saran Sereme daya daga cikin 'yan adawa

'Yan adawa ba su sha'awar iko a matsayin wucin gadi

Makonni biyu dai Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka ECOWAS ta bayar, wanda ta ce idan sojojin ba su mika iko ba, za ta sanya wa kasar takunkumi Jaridar ta kuma rawaito shugaban kungiyar kuma shugaban kasar Ghana John Dramani wanda yana bayyana cewa kungiyar tana bibiyan lamura a kasar amma shi kansa bai fadi wani abu mai kwari kan wannan batu ba.

A nata wajen, jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, wadda ita ma ta yi tsokaci kan wannan labarin, ta ce akwai alamun da ke nuna cewa zai dauki tsawon makonni da dama kafin a ce gwamnatin rikon kwaryarta zaunu har ta kama aiki gadan-gadan. Jaridar ta ce a yanzu haka dai babu wani dan adawar da ya nuna sha'awar karbar mukamin na shugabancin rikon, domin duk wanda ya yi haka ba zai sami damar tsayawa takara a zabukan na watan Nuwamba ba a yanzu haka dai jaridar ta ce ana yi wa lamarin na Burkina Faso kallon ko wata kila zai kasance mafarin guguwar sauyi tsakanin kasashen Afirka.

WHO na kiyasin sama da 13,000 sun mutu da Ebola

A yankin yammacin Afirka, cutar Ebola na nan na cigaba da yaduwa, mutane fiye da dubu 13 suka kamu da ita ya zuwa yanzu, in ji jaridar Süddeutsche Zeitung. Jaridar ta ce wannan ne bala'i mafi muni da aka taba gani a tarihin wannan cuta ta kuma rawaito wani dan Najeriya wanda ya kasance kwararre kan nazarin kwayoyin cututtuka, Oyewale Tomori yana danganta yaduwar cutar da matsalyar cin hanci da rashawar da ta addabi kasashen da cutarta fi tasiri.

Symbolbild Ebola Schutzanzüge Ärzte

Adadin masu kamuwa da Ebola na karuwa

A hirar da ya yi da jaridar shi ma ya amince cewa mahukunatn yankin ba su dauki matakan yaki da cutar a kan kari ba amma kuma matsala ce ta Afirka baki daya dole ne mahukunta su san haka su ba shi mahimmancin da ya ke bukata ba su cigaba da dogara da kasashen da sukaa cigaba ba, kuma matsalar ba rashin kudi ba ne, lallai kasashen Afirka na fama da talauci, amma matsalar abin da kasashen suka fgi baiwa fifiko ne wajen amfani da kudaden kasa, domin ba ya tsammanin akwai kasarda zata gaza sayen akalla safan hannu wa ma'aikata.

'Yan gudun hijira Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na bukatar tallafin gaggawa

Zentralafrikanische Republik

Mata da kananan yara suka fi wahala

Ita kuwa Jaridar die tageszeitung, ta yi labarin cewa kungiyoyin agaji na kasa da kasa da kuma masu ba da tallafi na fargabar karin matsalolin da za a fiskanta sakamakon adadin 'yan gudun hijira daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya inda ta ce kusan kashi 10 na al'ummar sun kauracewa matsugunnensu, yawancinsu na Kamaru, a yayin da wasu fiye da dubu 400 kuma ke watangaririya a cikin kasar, sun bar kasashensu ba su da wurin tsugunnawa, a dalilin haka ta ce babu wata alamar cewa za a sami damar tsugunnar da su cikin kwanaki kalilan, kuma dakarun hadin gwuiwa na MDD ta Turai ba za su iya taimakawa wajen dakatar da wannan matsalar su kadai ba kuma mafi mahimmanci, ba karamin kudi ne hukumar kula da 'yan gudun hijira na MDD wato UNHCR ke bukata domin baiwa.