Siriya za ta yi watsi da tallafi daga Turkiya | Labarai | DW | 13.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya za ta yi watsi da tallafi daga Turkiya

Wasu rahotanni na kafafan yada labarai na cewa akwai jirgin kayan agaji da ya nufi birnin na Aleppo daga Turkiya.

Libysche Flotte für Gaza

Dubban al'umma ne a yankin na Aleppo ke tsananin bukata ta tallafi

Gwamnatin kasar Siriya ta ce za ta yi watsi da duk wani kayan tallafi zuwa yankin Aleppo ba tare da an sanar da ita ba, ko ya bi ta hanyar Majalisar Dinkin Duniya, musamman kayan agaji da ya fito daga kasar Turkiya kamar yadda rahotanni na kafafan yada labarai suka nunar.

Ma'aikatar harkokin wajen Siriya ta ba da wannan bayani a cewar kamfanin dillancin labarai na SANA. Wannan jawabi dai na zuwa ne bayan da wasu rahotanni na kafafan yada labarai ke cewa akwai jirgin kayan agaji da ya nufi birnin na Aleppo daga Turkiya a ranar Talatan nan, abin da ke zuwa sa'oi bayan da shirin tsagaita bude wuta ya fara aiki bayan shiga tsakanin Amirka da Rasha.