Siriya: Turkiyya na shirin yi wa Afrin kawanya | Labarai | DW | 10.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya: Turkiyya na shirin yi wa Afrin kawanya

Dakarun kasar Turkiyya da ke samun goyon bayan wani bangare na 'yan tawayen Siriya, sun matso daf da birnin Afrin, inda suke a kimanin kilomita hudu da birnin da ke a matsayin cibiya ta Kurdawan kungiyar YPG.

Syrien FSA Operation Olivenzweig Afrin (picture alliance/AA/H. Nasir)

Dakarun Sojojin Turkiyya

Tun daga ranar 20 ga watan Janairu ne sojojin na Turkiyya suka ayyana kai hare-hare ta sama a yankin na Afrin da ke arewa maso yammacin kasar Siriya.

A halin yanzu dai sojojin na Turkiyya na kokarin yi wa birnin na Afrin kawanya, bayan da suke rike da kashi 60 cikin 100 na yankin a cewar Rami Abdel Rahmane shugaban kungiyar kare hakin bil-Adama ta OSDH a kasar ta Siriya.

Hare-haren na Turkiyya ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mayaka 370 na Kurdawan na YPG da kuma mayakan da ke mara musu baya sama da 340 a cewar wannan majiya. Sai dai rundunar sojojin kasar ta Turkiyya ta ce sojojinta 42 suka mutu a wannan yaki.