Siriya tace hare-haren da Rasha take Kai wa kan Is shiri ne na watanni. | Labarai | DW | 05.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya tace hare-haren da Rasha take Kai wa kan Is shiri ne na watanni.

Ma'aikatar harkokin wajen Siriya tace hare-haren jiragen sama da Rasha take Kai wa a kan 'yan kungiyar Is shiri ne da tuni aka tsara da zai kwashe watanni.

Walid al-Moualem

Walid al-Moulem Ministan kasashen wajen Syriya

Ministan harkokin wajen Siriya Walid al-Moulem a yayin da yake fadawa kafanin dallacin labaran kasar, yayi nuni da cewar baya raba da yan biyu cewar, matakin zai sami gagarumar nasara sabili da hadin gwiwar sojojin Rasha.

Tuni dai kasar Rasha ta samar da wata cibiya dake a kasar Iraki tattare da tallafin kasashen Siriya da kuma Iran don yin aiki tare tare da musayar muhimman bayanai a tsakanin su kan yakar kungiyar Isis dake a Siriya.