Siriya ta zargi Turkiyya da ta′addanci | Labarai | DW | 27.09.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya ta zargi Turkiyya da ta'addanci

Ministan harkokin wajen Siriya ya zargi kasar Turkiyya da kasancewa babbar mai daukar nauyin ta'addanci a kasarsa. Ministan ya yi wannan zargi ne a cikin faifan bidiyonsa da aka kunna a zauren taron MDD a ranar Asabar.

Walid al-Moallem wanda ya yi magana cikin fushi da bacin rai ya ce kiri-kiri Turkiyya ta datse hanyoyin samar da ruwa ga garuruwan Siriya da suka bijire wa mamayar da ta so ta yi musu.

Ministan ya kuma zargi Turkiyya da safarar 'yan ta'addar da take amfani da su a Siriya zuwa Libya, yana mai cewa Turkiyya na keta wa kasar Iraqi haddi wurin wannan safara. 

To sai dai wani jami'in Turkiyya a Majalisar Dinkin Duniya da bai so a ambaci sunansa ba ya ce dukkan zarge-zargen ba gaskiya bane, yana mai cewa gwamnatin Bashar al-Assad babu abin da take yi in ba hallaka mutanen Siriya ba, a don haka bai kamata a rinka ba ta damar yin soki-burutsu a taron Majalisar Dinkin Duniya ba.