Siriya: Jirgin sama ya rikito a yankin Idlib | Labarai | DW | 14.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya: Jirgin sama ya rikito a yankin Idlib

Wani jirgin gwamnatin kasar Siriya ya rikito a Aleppo da ke yankin Idlib sansanin da barkewar rikici ta sanya al'umma tserewa daga muhallansu.

Wannan al'amari na zuwa ne yayin da kasar Turkiyya ta aike da karin dakarun sojoji da makamai iyakokinta dake Kudu da kasar ta Siriya da nufin tunkarar dakarun gwamnatin Siriya domin karbe ragowar yankin da ke hannun 'yan tawaye bayan shekaru tara ana fafata yaki.

A wani sabon labarin kuma, wata hukumar sanya ido mai shalkwata a Birtaniya ta dora alhakin fadowar jirgin saman kan kasar Turkiyya.