Siriya: An kashe sojoji 4 a yankin Idlib | Labarai | DW | 03.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya: An kashe sojoji 4 a yankin Idlib

Sojojin Turkiyan na tallafawa mayakan da ke fada da rundunar gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad ne a yankin Idlib a lokacin da suka gamu da ajalinsu.

A kasar Siriya mai fama da yakin basasa, sojojin kasar Turkiya hudu ne suka mutu a yayin wani gumurzu a tsakanin rundunar gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad dana Turkiya a yankin Idlib a wannan Litinin, sanarwar da ma'aikatar tsaron kasar ta Turkiya ta fitar, ta ce lamarin ya auku ne a yayin da rundunar sojin kasar ta mayar da martani kan farmakin da rundunar gwamnatin Assad din ta kai a wani yanki da ta tsugunar da sojojinta a yankin na Idlib.

 Dakarun gwamnatin Siriya da ke samun goyon bayan Rasha a kokarin sake karbe ikon yankin na Idlib daga hannun babban kungiyar masu tayar da kayar baya na ci gaba da fuskantar tirjiya daga gwamnatin Turkiya da ke bayan wasu kunyiyoyin 'yan tawayen da ke neman hambarar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.