Shugabannin kasashe da dama za su hallara a taron MDD
September 19, 2025
Talla
Sama da shugabannin kasashe 140 ne za su hallara a birnin New York cikin makon gobe domin taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya.
Matsalar jinkai da ta addabi yankin Falasdinu za ta kasance a kan gaba a tattaunawar, shekaru biyu bayan kaddamar da farmakin Isra'ila a Zirin Gaza, wanda ya samo asali daga mummunan harin kungiyar Hamas na ranar 7 ga Oktoba, 2023.
Shugaba guda da ba zai halarci taron a Zahiri ba shi ne shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas, wanda Amurka ta hana biza tare da wadansu jami'ansa.
A karo na musamman, babban zauren ya kada kuri'a a ranar Juma'a domin bai wa Abbas damar yin jawabi ta hanyar bidiyo, yayin da jakadan Falasɗinu zai wakilce shi a cikin dakin taron.