Shugabanin Duniya na ci gaba da yin tir kan harin Brussels | Labarai | DW | 22.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabanin Duniya na ci gaba da yin tir kan harin Brussels

Shugaba Barack Obama na Amirka ya sha alwashin tallafa wa hukumomin Beljiyam domin ladaftar da duk wanda suke da hannu wajen hallaka sama da mutane 30 tare da jikkata karin sama da 160 Brussels.

Shugaban Amirkan yayin jawabin sa a Havana na Kyuba a lokacin da yake wata ziyara ya ce.

Muna nuna goyan baya garesu bisa yin Allah wadai kan wannan mummunan harin akan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, Zamu yi duk abin da ya zama wajibi wajen taimaka wa Beljiyam don gurfanar da duk wadanda suke da hannu, kana wannan wata tinatarwa ce ga Duniya cewar dole ne mu hadu guri daya.

Har yanzu dai shugabanin Duniya da kasashe na ci gaba da tofin Allah tsine kan harin na filin jigin saman Brussels a Beljiyam a inda Tuni Kungiyar IS ta ce ita ce ke da alhakin kai harin.