Shugaban Najeriya ya yi tir da harin da ya hallaka mutane takwas
October 28, 2012Talla
Shugaban ƙasar Najeriya Goodluck Jonathan ya yi tir da harin ƙunar baƙin wake cikin wata majami'a, a garin Kaduna da ke yankin arewacin ƙasar, wanda ya kira aikin ta'addanci. Harin ya yi sanadiyar hallaka aƙalla mutane takwas tare da jikata wasu sama da 100.
Shugaba Jonathan ya ce gwamnatin ƙasar ta ƙara zimma wajen kawo ƙarshen tashe tashen hankula da hare haren ta'addanci, tare da bayar da goyon bayan da ya dace ga jami'an, domin shawo kan matsalar.
Yanzu haka ƙura ta lafa a garin na Kaduna, inda aka ƙarfafa matakan tsaro, tare da tura jami'an tsaro cikin lunguna da kororo na birnin, amma hukumoki ba su kafa dokar hana fita ba.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas