Shugaban Najeriya ya sallami mashawarcinsa | Labarai | DW | 29.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Najeriya ya sallami mashawarcinsa

Goodluck Jonathan ya sallami Ahmed Gulak daga bakin aiki a matsayin daya daga cikin masu ba wa shugaban na Najeriya shawara.

A wani alamu na kazancewar rikicin siyasar Tarrayar Najeriya, Shugaba Goodluck Jonathan ya sallami babban mashawarcinsa a harkokin siyasa na gwamnatinsa Ahmed Ali Gulak.

Wata sanarwar kakakin fadar Reuben Abati ba ta ambato dalilin sallamar da ake kallon ta ba zata ba. To sai dai kuma Ahmed Gulak da ke zaman jigo a gwamnatin da kuma ke kan gaba ga kokarin neman sake tsayawa zabe na Jonathan ya fuskanci bacin ran mahukuntan na Abuja, bayan da ya yi gaban kansa wajen kafa reshen kungiyar Goodluck Support Group a jihar Akwa Ibom, abun kuma da ya jawo fushin gwamnan jihar Godswill Akpabio da shi ma ke zaman na kan gaba ga magoya bayan shugaban.

Gulak dai na zaman jami'i mafi karfin iko da ya rasa mukaminsa bayan kara ta'azarar rikicin tsaron da ya rikide zuwa na siyasa a Najeriya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal