Shugaban Najeriya ya ce za a gano 'yan matan da aka sace
May 5, 2014Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sha alwashin kubutar da 'yan mata 'yan marakanta 223 da ake zargin tsagerun kungiyar Boko Haram na garkuwa da su.
Shugaban ya bayyana haka a wannan Lahadi da ta gabata, yayin wata tattaunawa da manema labarai, wadda aka watsa kai tyaye ta tashoshin radiyo da talabijin. Ranar 14 ga watan jiya na Afrilu tsaregun dauke da makamai suka kai hari makarantar 'yan mata ta garin Chibok da ke Jihar Borno inda suka sace 'yan matan sama da 200. Ana nuna matukar damuwa a ciki da wajen kasar kan yadda gwamnatin Najeriya ke jan kafa na kubutar da 'yan matan.
A wani labarin, an daukaka matakan tsaro a Abuja fadar gwamnatin kasar ta Najeriya, yayin da ake fara taron tattalin arziki na Afirka cikin wannan mako.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal