Shugaban Najeriya ya bayyana arzikin da ya mallaka | Labarai | DW | 04.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Najeriya ya bayyana arzikin da ya mallaka

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo sun bayyana arzikin da suka mallaka

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayyana kaddara da ya mallaka da suka hada da kimanin kudin kasar Naira milyan 30, gidaje biyar da na ginin kasa biyu da gona wadda take dauke da shanu 270, tumaki 25 da tsintsaye da kuma itatuwa da aka dasa domin cin moriya.

Yayin da mataimakin Shugaba Yemi Osinbajo ya mallaki kudin kasar Naira milyan 94, da dala 900,000 da kuma Paund 19,000 gami da motoci uku da gidaje uku da kuma hannun jari a wasu kamfanonin a birnin Lagos.

Marigayi Shugaba Umaru Musa Yar'adua na Najeriya ke zama shugaban na farko a kasar da ya bayyana kaddarorin da ya mallaka lokacin da ya karbi madafun ikon kasar da ke yankin yammacin Afirka.